ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama mutane uku kafin aukuwar wannan harin, wadanda suke da niyyar kai hari kan masu ziyara humbaren na Kazimiyya.
A rana irin ta yau ce 25 ga watan Rajab Imam Musal Kazim(a) limami na 7 daga cikin limamai masu tsari daga iyalan gidan manzon Allah(s) ya yi shahada a zamanin sarki Haruna Rashid daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa a lokacin.
Wannan ranar a wajen mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (s) ranar makoki ne da kuma bakin ciki. Bayan aukuwan harin da ‘yan sa’o’ii ne Firai ministan kasar Iraki Mustafa Alkazimi ya ziyarci inda abin ya auku don ganewa idanunsa.
342/